An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, d…

Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, d…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na…

Bayanin hadisin: An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na…

Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, cewa su sun yawaita masa tambaya, sai ya yi fushi ya yi huɗuba sai ya ce: An bijiron da aljanna da wuta; ban taɓa ganin mafi alheri a cikin aljanna daga abinda na gan shi a yau ba.

Haka (bantaɓa ganin) mafi sharri mafi yawa daga abinda na gan shi a cikin wuta a yau ba, da kun ga abinda na gani, kuma kun san abinda na sani daga abinda na gan shi a yau da kafin yau da kun ji tsoro, tsoro mai yawa, da dariyarku ta ƙaranta, kuma kukanku ya yawaita. Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani yini bai taɓa zo wa sahabbansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - mafi tsanani daga wannan yinin ba, sai suka rufe kawunansu alhali gunji na kuka yana fita daga hanci saboda tsananin kuka. Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya miƙe sai ya ce: "Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi". Ya ce: Sai wancan mutumin ya miƙe, sai ya ce: Waye babana?

Ya ce: "Babanka shi ne wane". sai (aya) ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Maa'ida: 101].

Koyarwar hadisin: An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na…

Rukunan : ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah