Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الْعَبْدُ مِنْ رَبِّهِ وَهُوَ سَاجِدٌ، فَأَكْثِرُوا الدُّعَاءَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada.
Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.
Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · SABABAI NA AMSAR ADDU'A DA MASU HANA AMSARTA · FALALOLI DA LADUBBA