Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan…
Hasan ne kuma IngantacceAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ الْجَنَّةَ، فَقَالَ: «تَقْوَى اللهِ وَحُسْنُ الْخُلُقِ»، وَسُئِلَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ النَّارَ فَقَالَ: «الْفَمُ وَالْفَرْجُ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune:
Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u.
Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa.
Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta.
Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne:
Harshe da farji.
yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu.
Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI · HALAYE NAGARI · SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA · FALALOLI DA LADUBBA