Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahir…

Bayanin hadisin: Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahir…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance ba yana barin waɗannan addu'o'in ba lokacin da Ya yi yammaci da lokacin da ya wayi gari:

(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya), da kuɓuta daga masassara da masifu da tsanance-tsanance na duniya, da sha'awowi da fitintinu cikin Addini (a duniya da lahira) magaggauciya da majinkirciya.

(Ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwame) da shafe zunubai da ƙetare su.

(da lafiya) da kuɓuta daga aibuka, (a Addini na) daga shirka da bidi'o'i da saɓo, (da duniya ta) daga masifu da cuta da sharruka, (da iyalaina) matana da 'ya'ya na da 'yan uwana, (da dukiya ta) dukiyoyi na da aiki na.

(Ya Allah Ka suturta al'aurori na) da abinda ke cikina na aibuka da ɓaci da taƙaitawa Ka shafe zunubai na, (Ka amintar da tsorace -tsorace na) razani na da tsoro na.

(Ya Allah Ka kiyaye ni) Ka tunkuɗe bala'i daga gare ni daga abubuwa masu cutarwa da masifu, (ta gaba na da baya na, da dama na, da hagu na, da sama na) inda ya roƙi Allah Ya kiyaye shi ta kowane bangare: domin cewa masifu da aibuka kaɗai suna samun mutum ne kuma suna fuskantar sa daga ɗaya daga waɗannan ɓangarorin.

(Ina neman tsarinKa kada a kashe shi ni) shi ne a kamani bagtatan, in mutu ba tare da na sani ba (ta ƙarƙa shi na) sh ne in halaka ta kisfewa.

Koyarwar hadisin: Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahir…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah