Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya …
Ingantacce neTeburin Abun ciki :
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ أَكْثَرُ دُعَاءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللَّهُمَّ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً، وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً، وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita addu'a da addu'a gamammiya, daga cikinsu: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma Ka tsaremu azabar wuta", Ita ta tattaro kyau a duniya na arziki mai dadi, mayalwaci na halal, da mace ta gari, da da wanda ido zai yi farin ciki da shi, da hutu, da ilimi mai amfani, da makamancin hakan na abububuwan da ake so na halal, kyakkyawa a lahira na kubuta daga ukubobin kabari da tsayuwa da wuta, da samuwar yardar Allah, da rabauta da ni'ima madawwamiya, da kusanci ga Ubangiji Mai jin kai a lahira.
Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA