Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sar…
عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ شَيْءٌ أَكْرَمَ عَلَى اللهِ تَعَالَى مِنَ الدُّعَاءِ».
Bayanin hadisin: Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sar…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.
Koyarwar hadisin: Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sar…
- Falalar addu'a kuma wanda ya roƙi Allah, to, shi mai girmamashi ne, kuma mai tabbatarwa ne da cewa Shi (Allah) Mawadaci ne - tsarki ya tabbatar masa - ba a roƙon mabuƙaci, kuma cewa Shi Mai yawan ji ne kurma ba a roƙonsa, kuma cewa shi mai kyauta ne, marowaci ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai jin ƙai ne mai bushewar zuciya ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai iko ne gajiyayye ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Makusanci ne manisanci ba ya ji, da wanin haka na siffofin ɗaukaka da kyau na Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALAR ADDU'A
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa