Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wan…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wan…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Aminc…
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».
Bayanin hadisin: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Aminc…
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wadanne dabi'u ne na Musulunci suka fi? sai ya ambaci dabi'u biyu:
Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi.
na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.
Koyarwar hadisin: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Aminc…
- Kwadayin sahabbai akan sanin dabi'un da zasu anfanar a duniya da lahira.
- Sallama da ciyar da abinci suna daga mafifitan ayyuka; Dan falalarsu da bukatuwar mutane garesu a kowanne lokaci.
- Da wadannan dabi'un ne kyautatawa take taruwa da fada da aikatawa, kuma ita ce mafi cikar kyautatawa.
- Wadannan dabi'un a cikin abinda yake rataya ne na mu'amalantar musulmai a tsakaninsu, akwai wasu dabi'un na mu'amalantar bawa ga Ubangijinsa.
- Farawa da sallama abin kebancewa ne tsakanin musulmai, ba'a Farawa kafirai da sallama.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN SALLAMA DA NEMAN IZINI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa