‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da az…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > ‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala, da tsoro da rowa, da tsufa, da az…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala…

Bayanin hadisin: ‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala…

Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - «‌Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa» da fakewa gareKa, «‌Daga gajiyawa» rashin iko akan dabara mai amfani, «‌Da kasala» rashin samuwar niyyar yin aiki, gajiyayye ba ya iya yin wata dabara, mai kasala kuwa ba ta ma nufinta.

«‌Da tsoro» ta hanyar hanuwa daga gabatowa akan abinda aikata shi yake kamata, «‌Da rowa» da hana abinda bada shi yake wajaba, «‌Da tsufa» yawan shekarun da zai kai zuwa ga raunin jiki, «‌Da azabar ƙabari» Da sabubban da suke kaiwa zuwa ga hakan. «‌Ya Allah Ka bawa raina» Ka bata kuma Ka datar da ita ga «‌Tsron Allahnta» da aikata ɗa'a da barin saɓo, «‌Ka tsarkaketa» Ka tsarkaketa daga ƙasƙanci da munanan ɗabi'u, «‌Kaine mafi alherin wanda Ya tsarkaketa» babu wani mai tsarkaketa inbaKai ba, «‌Kaine majiɓincinta» Mai taimakonta kuma mai tsaya mata, «‌Kuma shugabanta» Mai jiɓintar al'amuranta, kuma Ubangijinta Mamallakinta kuma Mai ni'imtar da ita. «‌Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa daga ilimin da ba shi da amfani», kamar ilimin taurari da bokanci da tsafi, ko wanda ba zai yi amfani a lahira ba, ko ilimin da ba za’a yi aiki da shi ba, «‌Da zuciyar da bata risinawa» gareKa, kuma bata ƙanƙar da kai, kuma bata nutsuwa, bata nutsuwa saboda ambatanKa, «‌Da ran da baya ƙoshi» ba ya wadatuwa da abinda Allah Ya ba shi kuma Ya azurta shi daga halal mai tsarki, «‌Da addu'a» abar juyarwa «‌wacce ba'a amsa mata».

Koyarwar hadisin: ‌Ya Allah ! Ina neman tsarinKa daga gajiyawa, da kasala…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah