Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa…
عَنْ أَبِي حَمْزَةَ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ -خَادِمِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ- عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ، حَتَّى يُحِبَّ لِأَخِيهِ مَا يُحِبُّ لِنَفْسِهِ»
Bayanin hadisin: Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.
Koyarwar hadisin: Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa…
- Wajabcin so wa mutum ga ɗan'uwansa abinda yake so wa kansa; domin kore imani ga wanda ba ya son abinda yake so ga ɗan'uwansa yana nuni akan wajabcin hakan.
- 'Yan uwantaka a tafarkin Allah sama take akan 'yan uwantaka ta nasaba, to hakkinta shi ne mafi wajaba.
- Haramcin dukkan abinda yake kore wannan soyayyar na maganganu da ayyuka, kamar algus da raɗa da hassada da ta'addanci akan ran musulmi ko dukiyarsa ko mutuncinsa.
- Yin anfani da wasu daga lafuzza masu kwaɗaitarwa akan yin aiki; saboda faɗinsa: "Ga ɗan'uwansa".
- Karmani - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Kuma yana daga cikin imani ya ki wa ɗan'uwansa abinda yake ki wa kansa na sharri, amma bai ambace shi ba; domin son abu mai lazimtar kin kishiyarsa ne , to hakan ya isu akan barin fadinsa.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah