Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta t…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَوْ أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَوَكَّلُونَ عَلَى اللهِ حَقَّ تَوَكُّلِهِ لَرَزَقَكُمْ كَمَا يَرْزَقُ الطَّيْرَ تَغْدُو خِمَاصًا وَتَرُوحُ بِطَانًا».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.
Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN AYYUKAN ZUCIYA · FALALOLI DA LADUBBA