Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na …
Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita…
Bayanin hadisin: Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita…
Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.
Koyarwar hadisin: Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita…
- Falalar Suratul Ikhlas, kuma ita tana daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.
- Halaccin karatu a sallar tsayuwar dare koda da ayoyi kaɗan ne da kuma maimaita su, da rashin ƙaranta hakan.
- AlMaziri ya ce: An ce: Ma'anarsa: Cewa Alƙur'ani yana da ɓangarori uku; Kissoshi da hukunce-hukunce da kuma siffofin Allah - Maɗaukakin sarki -, {Ka ce Shi ne Allah Makaɗaici} mai tacewa ce - yana nufin ga siffofin Allah -, dan haka ita ce ɗaya bisa uku, kuma wani yanki daga cikin yankuna uku. Kum an ce: Ma'narsa: Cewa ladan karantata ana ninka shi da gwargwadan ladan karatun ɗaya bisa uku na Alƙur'ani ba tare da ninkawa ba.
Rukunan :
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA
· FALALOLI NA ALƘUR'ANI
· FALALOLI NA SURORI DA AYOYI
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah