Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min s…

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min s…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai…

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ قَالَ: خَرَجَ مُعَاوِيَةُ عَلَى حَلْقَةٍ فِي الْمَسْجِدِ، فَقَالَ: مَا أَجْلَسَكُمْ؟ قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ، قَالَ آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟ قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَمَا كَانَ أَحَدٌ بِمَنْزِلَتِي مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقَلَّ عَنْهُ حَدِيثًا مِنِّي: وَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَى حَلْقَةٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: «مَا أَجْلَسَكُمْ؟» قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ وَنَحْمَدُهُ عَلَى مَا هَدَانَا لِلْإِسْلَامِ، وَمَنَّ بِهِ عَلَيْنَا، قَالَ: «آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟» قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: «أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَلَكِنَّهُ أَتَانِي جِبْرِيلُ فَأَخْبَرَنِي أَنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُبَاهِي بِكُمُ الْمَلَائِكَةَ».

Bayanin hadisin: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai…

Mu'awiya Dan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da su - ya fito ga wata halƙa a cikin Masallaci, sai ya tambayesu akan wanne abu ne suka taru? sai suka ce: Muna ambatan Allah, sai ya sa suka rantse, Allah Ya yarda da shi - cewa su ba su yi nufin komai da taruwarsu ba sai zikiri, sai suka rantse masa, Sannan ya ce da su: Lallai ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku da kuma kokwanto a gaskiyarku ba, sannan ya bada labari game da matsayinsa ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi babu wani mutum dake da matsayin kusancin sa daga gare shi; dan kasancewar Ummu Habiba 'yar uwarsa ce kuma matar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ce-, dan kuma kasancewarsa daga marubutan wahayi, tare da hakan to shi mai ƙarancin riwaya ne ga hadisai. Sai ya zantar da su cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito wata rana daga gidansa, sai ya samesu a zaune a cikin masallaci, suna anbaton Allah suna gode masa akan shiryar da su da ya yi , ya kuma ni’imta su da shi, sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye su ya kuma rantsar da su da irin abinda Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya aikata tare sahabban sa. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa musu sababin tambayar sa gare su da kuma rantsar da su da ya yi: Cewa mala'ika Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya zo masa sai ya ba shi labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku, kuma yana bayyanar da falalarku gare su, kuma yana nuna musu kyakkyawan ayyukanku, Yana yabon ku a gurin su.

Koyarwar hadisin: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai…

Rukunan : FALALOLI · FALALAR ILIMI · FALALOLIN ZIKIRI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah