Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba
عن جُبَير بن مُطْعِم رضي الله عنه أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعُ رَحِمٍ».
Bayanin hadisin: Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yanke abin da yake wajaba daga 'yan uwansa na haƙƙoƙi, ko ya cutar da su ya munana musu, to, ya cancanci ba zai shiga aljanna ba.
Koyarwar hadisin: Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba
- Yanke zumunci laifi ne daga manyan laifuka.
- Sa da zumunci yana kasancewa ne gwargwadon abin da aka yi sabo a kansa, yana banbanta da banbantar wurare da zamaninnika da mutane.
- Sa da zumunci yana kasancewa ne da ziyara da sadaka, da kyautatawa garesu, da duba marasa lafiya, da umartarsu da aikin alheri, da hanasu daga abin ƙi, da makamancin hakan.
- A duk lokacin da yanke zumuci ya zama da mafi kusanci, to, zai zama ya fi tsananin laifi.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN SA DA ZUMUNCI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah