Addu'a ita ce ibada

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Addu'a ita ce ibada

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Addu'a ita ce ibada

عن النعمان بن بَشِير رضي الله عنه قال: سمعت النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الدُّعَاءُ هُوَ الْعِبَادَةُ»، ثُمَّ قَرَأَ: «{وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ} [غافر: 60]».

Bayanin hadisin: Addu'a ita ce ibada

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya.

Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.

Koyarwar hadisin: Addu'a ita ce ibada

Rukunan : FALALOLI · FALALAR ADDU'A · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah