‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > ‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi

Hasan ne da wani Sanadin

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: ‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan w…

Bayanin hadisin: ‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan w…

An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne, ɗayan kuma malamai ne, wanene yafi a cikinsu?

Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Falalar masanain ilimummukan shari'a mai yin aiki da su kuma mai koyar da su akan mai yin ibada wanda ya kaɗaita ga ibada tare da da cewa ya san abinda ya wajaba akansa na ilimi kamar falalarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗaukakarsa akan mafi koma baya daga cikin sahabbai Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sababin hakan da cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da mala'ikunSa cikin maɗauka al'arshi, da waɗanda ke cikin sammai na sauran mala'iku, da ma'abota ƙasa na aljanu da mutane da dukkanin dabbobi, har tururuwa a gidanta a cikin ƙasa, har kifin da ke cikin kogi; dan ya haɗa dabbobin sarari (tudu) da kogi, dukkanin waɗannan sunayin addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane ilimummukan Addinin da a cikinsu akwai tsiran mutane da kuma rabautarsu.

Koyarwar hadisin: ‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan w…

Rukunan : FALALOLI · FALALAR ILIMI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah