Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi w…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi w…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi
Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i d…
Bayanin hadisin: Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i d…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.
Koyarwar hadisin: Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i d…
- Kwaɗaitarwa akan dawwama akan zikiri dan yawaita dashen aljanna.
- Falalar al'ummar musulmi; inda (Annabi) Ibrahim - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya isar mata da sallama.
- Kwaɗaitarwa (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - ga al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cikin yawaitawa daga ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Malam al-Ɗaibi ya ce: Aljanna ...?, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya samar mata da bishiyoyi da katangu da falalarsa gwargwdan ayyukan masu aiki; kowane mai aiki akwai abinda ya keɓanta da shi saboda aikinsa, sannan cewa Shi - Allah Maɗaukakin sarki - yayin da Ya sawwaƙa masa dan abinda Ya halicce shi saboda shi na aiki dan ya samu lada da hakan sai Ya sanya shi kamar mai dasa waɗancan bishiyoyin.
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN ZIKIRI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah