Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, fac…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, fac…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da…
Bayanin hadisin: Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.
Koyarwar hadisin: Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da…
- Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa bane akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin kafin ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
- Hasara mai faruwa garesu a ranar alƘiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin da saɓon Allah.
- Wannan tsoratarwar idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba (yi da wani) da annamimanci da wasunsu?!
Rukunan :
FALALOLI
· FALALOLIN ZIKIRI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye