Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, …

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, s…

عن أبي أيوب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، عَشْرَ مِرَارٍ كَانَ كَمَنْ أَعْتَقَ أَرْبَعَةَ أَنْفُسٍ مِنْ وَلَدِ إِسْمَاعِيلَ».

Bayanin hadisin: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, s…

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ma’ana: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa. To, duk wanda ya maimaita wannan zikirin a rana sau goma, to, yana da lada misalin ladan wanda ya gusar da bauta daga bayi huɗu cikin zuriyar [Annabi] Isma’il Ɗan [Annabi] Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma ya keɓance zuriyar [Annabi] Isma’il ne amincin Allah ya tabbata a gare shi domin sun fi waɗanda ba su ba.

Koyarwar hadisin: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, s…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN ZIKIRI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah