Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa,…

Bayanin hadisin: Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa,…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya fada, ban da Hai'ala biyu, cewa ya ce a bayansu: Babu dabara ba ƙarfi sai ga Allah.

Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku.

Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta.

Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

Koyarwar hadisin: Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa,…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FALALOLI · FALALOLIN ZIKIRI · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · KIRAN SALLAH DA IƘAMA · FALALOLI DA LADUBBA · Imani da Ranar Lahira

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah