Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gare…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na muamalat > Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gare…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai…

Bayanin hadisin: Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai…

Abu Musa Al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da shi akwai wasu jama'a daga kabilarsa, manufarsu ita ce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya basu rakuman da zasu hau; dan samun damar fita yaki, sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyin su ba, ba shi da abinda zai dauki nauyinsu da shi, sai suka koma suka zauna tsawon wani lokaci, sannan wasu rakuma uku suka zo wa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, sai ya aika musu, sai sashinsu ya cewa sashi: Allah ba zai yi mana albarka a wadannan rakuma ukun ba; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyinmu ba, sai suka zo masa suka tambaye shi , sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Wanda ya dauki nauyinku Shi ne Allah - Madaukkain sarki -; domin cewa Shi ne Mai datarwa kuma Mai azirtawa, kadai ni sababi ne wanda hakan ya gudana ta hannuna, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na rantse da Allah, idan Allah Ya so ba na rantsuwa akan wani abu da aikata shi ko na bar shi, kuma in ga wanin wannan abinda na rantse akansa shi ne mafi alheri, sai na aikata abinda yafin kuma in bar wanda na rantse akansa din, kuma in yi kaffarar rantsuwa ta.

Koyarwar hadisin: Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai…

Rukunan : FIƘHU NA MU'AMALAT · RANTSUWA DA BAKANCE · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah