Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama
Musulunci > Ha > Hadith > Haddodi > Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa…
Bayanin hadisin: Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.
Koyarwar hadisin: Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa…
- Sata tana daga cikin manyan zunubai.
- Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya iyakance uƙubar ɓarawo, ita ce yanke hannunsa; kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Barawo da ɓarauniya to ku yanke hannayensu} [al-Ma'ida: 38], kuma sunnah ta bayyana sharuɗɗan wannan yankewar.
- Abin nufi da hannu a cikin hadisin shi ne yanke tafi daga gaɓarsa tsakaninsa da tsakanin damtse.
- Daga hikima a cikin yanke hannun ɓarawo, (akwai) kiyaye dukiyoyin mutane, da tsawatar da waninsa (ɓarawon) cikin masu ta'addanci.
- Dinari awo ne na zinare, kuma ya yi daidai a yanzu da (4.25 KG) awon 24; to ɗaya bisa huɗu na dinari ya yi daidai da Gram da wani abu.
Rukunan :
HADDODI
· HADDIN SATA
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah