Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga ciki…
عَنِ ابنِ مَسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَحِلُّ دَمُ امْرِئٍ مُسْلِمٍ إِلَّا بِإِحْدَى ثَلَاثٍ: الثَّيِّبُ الزَّانِي، وَالنَّفْسُ بِالنَّفْسِ، وَالتَّارِكُ لِدِينِهِ المُفَارِقُ لِلْجَمَاعَةِ».
Bayanin hadisin: Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga ciki…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa jinin musulmi haramun ne, sai dai idan ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi'un nan uku: Na farko: Wanda ya faɗa cikin alfashar zina, alhali ya riga ya yi aure da ƙulla ingantaccen ɗaurin aure, to sai kashe shi ta hanyar jifa ya halatta. Na biyu: Wanda ya kashe tsararren rai da aka hana kashewa ba tare da wani haƙƙi ba, to sai a kashe shi da sharuɗɗansa. Na uku: Wanda ya fita daga cikin jama'ar muslmai; ko dai ta hanyar barin addininsa gabaɗayansa ta hanyar yin ridda, ko wanda ya bari ba tare da ridda ba ta hanyar barin sashinsa kamar 'yan tawaye, da 'yan fashi, da mayaƙa cikin Khwarij da wasunsu.
Koyarwar hadisin: Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga ciki…
- Haramcin aikata waɗannan ɗabi'un uku, kuma wanda ya aikata ɗaya daga cikinsu ya cancanci uƙubar kisa; ko dai kafirci, shi ne yin ridda daga Musulunci, ko kuma haddi, sune: Bazawarin da ya yi zina, da wanda ya yi kisa da gangan.
- Wajabcin kiyaye mutunci da kuma tsarkake shi .
- Wajabcin girmama musulmi, kuma jininsa a tsare yake.
- Kwaɗaitarwa akan lazimtar jama'ar musulmai da kuma rashin rabuwa da su.
- Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda wani lokaci zancensa yake zuwa da rarrabewa; domin rarrabewar tana taƙaita mas'aloli kuma tana tattarosu, kuma shi ne mafi saurin haddacewa.
- Allah Ya shara'anta haddodi; dan tsawatar da masu laifi, da kuma kare zamantakewa da kiyayewa daga manyan laifuka.
- zartar da waɗannan hukunce hukuncen ya rataya ne akan shugaba ne kadai.
- Dalilan dake sa a yi kisa sun fi uku, sai dai basa fita daga wadannan ukun, Ibnul Arabi al-Maliki ya ce: Ba sa fita daga waɗanannan ukun ta kowane irin hali, domin duk wanda ya yi asiri, ko ya zagi Annabin Allah to ya kafirta, shi ya shiga cikin wanda ya bar addininsa.
Rukunan :
HADDODI
· HUKUNCE-HUKUNCEN HADDODI
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah