Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Ya Manzon Allah, shin ina da lada akan yayan Abu Salamah da zan ciyar dasu, kuma bana bari…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أم سلمة رضي الله عنها ، قالت: قلت: يا رسول الله، هل لي أجرٌ في بني أبي سلمة أن أُنْفِقَ عليهم، ولستُ بتاركتهم هكذا وهكذا إنما هم بَنِيَّ؟ فقال: «نعم، لك أجرُ ما أنفقتِ عليهم».
Ummu Salamah, Allah ya yarda da ita, ta ce wa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Shin ina da wani lada a ciki na ciyar da ‘ya’yana daga Abu Salamah kuma na isar musu, kuma ban bari su watse a cikin neman guzuri ba? Ko kuwa babu wani sakamako a wurina saboda na yi ta ne da tausayi saboda 'ya'yana ne? Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gaya mata cewa za a ba ta ladan ciyarwa a kan su.
Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · CIYARWA · FIƘHU DA USULU