Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata warak…
Musulunci > Ha > Hadith > Likitanci da magani da ta waida ta sharia > Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata warak…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, K…
Bayanin hadisin: Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, K…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.
Koyarwar hadisin: Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, K…
- Mai warkarwa Shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -, amma likita da magani to su biyun sabubba ne basa anfanarwa kuma ba sa cutarwa sai da izinin Allah.
- Gaida mara lafiya yana daga haƙƙoƙi tsakanin musulmai, hakan cancanta ga iyalai.
- Kwaɗaitarwa ga wanda ya ziyarci mara lafiya ya yi masa wannan addu'ar mai albarka waccea aka ruwaito.
- Daga shiryrwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yin magani da ruƙya ta shari'a da Alƙur'ani da kuma addu'o'i masu tsarki, saboda haka tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana yi wa kansa ruƙya idan ya yi rashin lafiya, haka nan yana yi wa wanda ya yi rashin lafiya daga iyalansa da wasunsu ruƙiyya.
- Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa yi wa mara lafiya addu'ar waraka tare da abinda ke cikin rashin lafiya na kankare zunubai da lada kamar yadda hadisai suka zo da hakan ya rikitar, to amsa ita ce: Lallai addu'a ibada ce, kuma bata kore lada da kuma kaffara; domin cewa su suna samuwane a farkon rashin lafiyar da kuma haƙuri a kanta, mai addu'a yana tsakanin kyawawa biyu: Kodai abin nufinsa ya samu, ko kuma a canja masa da jawo wani anfanin ko tunkuɗe cuta, kowanne daga cikinsu daga falalar Allah ne.
Rukunan :
LIKITANCI DA MAGANI DA TA-WAIDA TA SHARI'A
· RUƘYA IRIN TA SHARI'A
· LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN DUBA MARA LAFIYA
· FIƘHU DA USULU
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa