Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda y…
Musulunci > Ha > Hadith > Abibciccika da abubuwan sha > Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda y…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya ruwaito shi, shi kuwa Bukhari ya ruwaito jimla ta karshe ne ta Hadisin
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abin…
Bayanin hadisin: Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abin…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.
Koyarwar hadisin: Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abin…
- Illar haramta giya shi ne maye, dukkan abinda yake sa maye daga kowanne nau'i ya kasance to haramun ne.
- Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta giya; dan abinda ta ƙunsa na cututtuka da ɓarna masu girma.
- Shan giya a cikin aljanna yana daga cikar jin daɗi da cikar ni'ima.
- Wanda bai kame kansa daga shan giya a duniya ba Allah Zai haramta masa shan ta a cikin aljanna. Sakamako yana zuwa ne daga jinsin aiki.
- Kwaɗaitarwa akan gaggawar tuba daga zunubai kafin mutuwa.
Rukunan :
ABIBCICCIKA DA ABUBUWAN SHA
· ABUBUWAN SHA NA HARAMUN
· FIƘHU DA USULU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa