Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah …
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah …
Wanda ya ruwaito hadisin: Ibnu Khuzaimah da Dar Al-Kutni da Baihaki ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sa…
Bayanin hadisin: Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sa…
Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).
Koyarwar hadisin: Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sa…
- Faɗinsa: (Yana daga sunnah): Yana nufin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to shi yana da hukuncin Raf'u, wato wanda aka danganta shi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- An so mai kiran sallah a cikin kiran sallar Asuba ya ce bayan ya faɗi: Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira): Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri), sau biyu; domin sallar Asuba a lokacin da mutane suke bacci ne a cikinsa, zasu tashi daga bacci zuwa sallah, sai aka keɓanci sallar Asuba da hakan banda sauran sallolin.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHU DA USULU
· KIRAN SALLAH DA IƘAMA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah