Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wan…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wan…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika y…
Bayanin hadisin: Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika y…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi .
wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.
Koyarwar hadisin: Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika y…
- Kwaɗaitar da musulmai akan taimakekeniya akan ayyukan alheri.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikin wannan Hadisin a kwai kwaɗaitarwa akan kyautatawa ga wanda ya aikata wata maslaha ga musulmai, ko ya tsaya da wani al'amari daga abubuwan da ya shafesu.
- Ka'ida gamammiya: Cewa wanda ya taimaki wani mutum a cikin aikin ɗa'a daga ayyukan ɗa'a ga Allah to yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da an rage wani abu daga ladansa ba.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· JIHADI
· FIƘHU DA USULU
· FALALAR JIHADI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah