Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna…
Bayanin hadisin: Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.
Koyarwar hadisin: Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna…
- Haramcin kashe kafirin amana da zimmi da musta'aman (wanda aka ba shi amincin ɗan wani lokaci) daga kafirai, kuma cewa hakan babban laifi ne daga manyan laifuka.
- Kafirin amana: Shi ne wanda aka yi alƙawari da shi daga kafirai a kan ya zauna a garinsa ba zai yaƙi musulamai ba su ma ba za su yaƙe shi ba. Zimmi kuma: Shi ne wanda ya zauna a garin musulmai ya ba da jizya. Musta'aman kuma: Shi ne wanda ya shiga garin musulmai a kan alkawari da aminci na wani ƙayyadajjen lokaci.
- Gargaɗi daga ha'intar alƙawurra (da aka ƙulla) tare da wanin musulmai.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· JIHADI
· FIƘHU DA USULU
· HUKUNCE-HUKUNCEN KAFIRAN AMANA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
اللهم صل على محمد
Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad