Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na muamalat > Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana…

Bayanin hadisin: Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}.

Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.

Koyarwar hadisin: Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana…

Rukunan : FIƘHU NA MU'AMALAT · ALƘALANCI · RANTSUWA DA BAKANCE · ƘARARRAKI DA SHEDU · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah