Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Kar ka saye shi, kar ka dawo da sadakar da ka yi, ko da kuwa dirhami daya aka sayar maka, …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: «حَمَلْتُ على فرس في سبيل الله، فأضاعه الذي كان عنده، فأردت أن أشتريه، وظننت أنه يبيعه بِرُخْصٍ، فسألت النبي صلى الله عليه وسلم ؟ فقال: لا تَشْتَرِهِ، ولا تعد في صدقتك؛ فإن أَعْطَاكَهُ بِدِرْهَمٍ؛ فإن العَائِدَ في هِبَتِهِ كالعَائِدِ في قَيْئِهِ».
Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya taimaki wani mutum akan jihadi a tafarkin Allah. sai ya bashi doki ya yi yaki a kansa, sai mutumin sai mutumin ya kasa ciyar da dokin, ba ya kula da shi, ya gajiyar da shu, har ya rame yayi rauni. Sai Umar yayi niyyar sayen dokin don ya san zai yi sauki sabo da ramewa da raunin da ya yi, sai dai bai yi cinikin dokin ba sai da ya shawarci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- game da haka,sai Annabi ya hana shi sayen dokin komai araharsa, saboda wannan abu ne da aka bayar don Allah, kar ka damu da shi,sai ya zama kamar ka dawo da wani bangare na abin da ka bayar ne, don ka riga ka bayar, kuma an kankare zunubanka, datti ya fita daga gare ka, bai kamata ya komo gareka ba, wannan shi yasa aka ambaci cinikin da suna kome duk da cewa saye zai yi.
Rukunan : FIƘHU NA MU'AMALAT · KYAUTA DA KYAUTA · FIƘHU DA USULU