Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan akurkin Da ki, kuma tasanya Mafi m…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan akurkin Da ki, kuma tasanya Mafi m…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

Teburin Abun ciki :

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan…

عن أم سلمة رضي الله عنها مرفوعاً: «جاءت امرأة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، إن ابنتي توفي عنها زوجها، وقد اشتكت عينها أفَنَكْحُلُها؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : لا -مرتين، أو ثلاثا-، ثم قال: إنما هي أربعة أشهر وعشر، وقد كانت إحداكن في الجاهلية ترمي بالبَعْرَةِ على رأس الحول».
فقالت زينب: كانت المرأة إذا توفي عنها زوجها: دخلت حفشا، ولبست شر ثيابها، ولم تَمَسَّ طيبا ولا شيئا حتى تمر بها سنة، ثم تؤتى بدابة -حمار أو طير أو شاة- فتَفْتَضُّ به! فقلما تفتض بشيء إلا مات! ثم تخرج فتُعطى بعرة؛ فترمي بها، ثم تراجع بعد ما شاءت من طيب أو غيره».

Bayanin hadisin: Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan…

Musulunci ya zo, kuma ka gusarwa Mutane dukkan kazantar Jahiyya, Musamman ma ga Mata, domin suna munana Mu'amala ga Matan kuma suna Zaluntarta, Sai Musulunci ya kwato mata hakkinta, to a cikin wannan Hadisin wata Mata ta zo tana neman fatawar Annabi cewa Mijin Diyarta ya Mutu, kuma zata yi masa Iddakuma Mai Idda bata Kwalliya, saidai kuma tana fama da ciwon Ido, shin anyi mata rangwame da ta yi amfani da Kwalli ne? sai Annabi ya ce Mata AA kuma yana mai maimaita mata hakan, sannan ya karanta mata ganin tsawon muddar Iddar tata, wanda Mace zata yi Idda ne fa don Alfarmar Mijinta tsawon wata hudu da kwana goma, yanzu ba zata iya jurewa ba a wanna Dan lokacin kadan wanda ba shi da wani tsawo? kuma Mata sun kasance a Jahiliyya, suna shiga Idda ne cikin Dan wani karamin Daki kamaer wani ramin kura, kuma su daina kwalliya, da saka turare, haka ma yin amfani da ruwa, da kuma cudanya da Mutane, sai Mace tayi cidin cidin da Dauda da kazanta na rashin wanka, kuma ba ita babu Mutane, shekara guda cur, to idan ta gama gama iddar sai a bata kashin Rakumi tayi jifa da shi, wannan shi yake nuna cewa duk wannan wahalar da ta shiga babu wani abu na kimantawa da ta yi na wannan abu da tayi don Mijinta sai wannan wulakantaccen abun (KashinRakumi) sa i Musulunci ya zo ya canza Mata waccan wahala da wata Ni'ama, da kuma wancan tsananin, kuma Sannan yaya ba zata iya hakuri ba da kwallin Idonta, to don haka babu Rangwame a gareta, don kada hakan ya zama tsani izuwa bude kofar Ado ga Mai Takaba.

Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · IDDA · FIƘHU DA USULU

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 17.3 / 29.5
Haske 93%
Wata Sabo a cikin kwana 12
سبحان الله وبحمده Tsarkin Allah da godiyarSa

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah