To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida akan zalinci

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na zamantakewar iyali > To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida akan zalinci

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, kuma yana da Lafuza da dama

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida…

Bayanin hadisin: To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida…

Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa mahaifiyarsa Amrah 'yar Rawaha - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi babansa wata kyautar da zai bawa ɗanta daga dukiyarsa, sai ya yi nauyi ya jinkirtata har shekara, sannan ya ga ya kamata ya amsa mata abinda ta nema sai ya bawa ɗansa Nu'uman kyauta, sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sheda akan abinda ka bawa ɗana, sai babana ya riƙe hannuna ni kuma a wannan lokacin ina ƙaramin yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in sakaka shaida akan abinda na bawa ɗanta kyauta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya kai Bashir, shin kana da wani ɗan ne banda wannan? Ya ce: Eh. Sai ya ce: Shin dukkansu ka ba su kwatankwacin wannan? Ya ce: A'a. Ya ce: To kada ka sa ni shaida, domin cewa ni ba na shaida a kan zalinci. A riwayar Muslim ya ce yana mai zarginsa: Sai dai ka sa wanina ya yi shaida a kan wannan zalincin.

Koyarwar hadisin: To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida…

Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · HUKUNCE-HUKUNCEN ABIN HAIHUWA · FIƘHU DA USULU · CIYAR DA 'YA'YA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah