Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi

Ingantacce ne ta wani bangaren

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya…

Bayanin hadisin: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya…

Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.

Koyarwar hadisin: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah