Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin ab…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.
Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · TSARIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBBA A GARESHI WAJEN YIN ZIKIRI · FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · ZIKIRAI NA SHIGA DA FITA DAGA GIDA · FALALOLI DA LADUBBA