Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) ak…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) ak…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya…

Bayanin hadisin: Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba.

domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -.

Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware.

Idan ya yi alwala sai ya warware.

Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.

Koyarwar hadisin: Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA · FIƘHU DA USULU · ALWALA · FALALAR ALWALA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah