’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin…

Bayanin hadisin: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Ya yi addu'a da wata addu'a wacce ya haɗo a cikinta tushen manyan ɗabi'u waɗanda aka aiko shi dan cikasu; su ne gyara Addini, da duniya, da lahira, sai ya nemi shayarwar gyaran waɗannan abubuwan masu tattarowa guda uku a cikin wannan taƙaitaccen lafazin, sai ya fara da gyaran Addini da shi ne (za'a samu) gayaran halin gidaje biyun (duniya da lahira) sai ya ce:

(Ya Allah Ka gyara mini Addini na) shi ne Ka datar dani da tsayuwa da ladubbansa ta cikakkiyar fuska mafi cika.

(Wanda shi ne kashin bayan al'amarina) mai kiyayewa ga dukkan al'amurana, idan Addinina ya ɓaci to al'amurana sun ɓaci, na taɓe na yi asara, kuma cewa gyaruwar Addini abin nema baya cika sai da gyaruwar duniya , sai ya ce:

(Ka gyara mini duniyata) ta hanyar lafiyar jiki da aminci, da arziƙi, da mata ta gari, da zuriya kyakkyawa da abinda nake buƙatuwa zuwa gare shi, kuma ya zama na halal, mai taimako akan yi maKa biyayya, sannan ya ambaci uzuri a cikin tambayarsa gyaranta; shi ne ya ce:

(Wacce a cikinta rayuwata ta ke) da wurin rayuwata da zamanin rayuwata.

(Kuma ka gyara min lahirata wacce a cikinta ne makomata take) da komawata zuwa haɗuwa da Kai, hakan da gyaruwar ayyuka, da datarwar Allah ga bawa akan ibada da ikhalasi, da kyakkyawar cikawa.

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya jeranta lahira bayan duniya; domin ta farko ita ce tsanin gyaran ta biyu, wanda ya daidaita a duniyarsa daidai da abinda Allah yake so, to lahirarsa ta daidaita kuma ya azirta a cikinta.

(Ka sanya rayuwa) da tsawon rayuwa (ƙari gareni a kowane alheri) da zan yawaita ayyuka na gari a cikinta.

(Ka sanya mutuwa) da gaggautota (hutu gareni daga kowane sharri) da fitina da jarraba da ibtila'i da saɓo da rafkana, da kuma kuɓuta daga wahalar duniya da baƙin cikinta, da samun hutu.

Koyarwar hadisin: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah