Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa …

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da…

Bayanin hadisin: Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita daga wurin matarsa Uwar muminai Nana Juwairiyya - Allah Ya yarda da ita - a farkon yini lokacin da ya yi sallar Asuba, alhali ita tana zaune a wurin sallarta, sannan ya dawo bayan rana ta ɗaga lokacin sallar walaha, alhali ita ba ta gushe ba tana zaune a wurinta, sai ya ce: Shin baki gushe ba akan halin da na barki akansa? Ta ce: Eh, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Haƙiƙa a bayanki na faɗi wasu kalmomi huɗu, kuma na maimaita su sau uku, da za'a auna da abinda kika faɗa a gaba ɗayan lokacin da kike a zaune a cikinsa da sun rinjaye su: (Tsarki ya tabbata ga Allah) da tsarkakarSa daga dukkan tawaya, (da godiyarSa) inda Yake da kyakkyawan yabon da Ya shiryar ga hakan, (adadin halittarSa) waɗanda babu mai iya iyakancesu sai Allah, (da yardar kanSa) da gwargwadan abinda Ya yardar maSa ga wanda Allah Ya yarda da shi daga bayinSa kuma shi wani abu ne ba’a kewaye shi da sani , (da awon Al’arshin sa) wanda shi ne mafi girman halittu kuma mafi nauyinsu, (da tawadar kalmominSa) kuma kalmomin Allah ba sa taƙaituwa kuma ba sa ƙarewa; wannan yana gemawa kuma yana ƙunsar rabe-raben uku; domin tawadar kalmominSa - tsarki ya tabbatar maSa - babu karewa ga iyakarta, ko ga siffarSa ko ga adaddinsa, sai dai abin nufi: Kai matuka da shi a yawa; domin a farko ya ambaci abinda kirge mai yawa na adadin halitta yake iyakance shi , sannan ya hau zuwa abinda shi ne mafi girma daga nan kuma ya bayyanar daga gare shi da yardar kanSa, sannan awon mafi girman halittu shi ne al'Arshi; na farkon dan kirgawa ne da kuma yawa, na biyun kuma da siffa ne da kuma kaifiyya, na uku dan girma da kuma nauyi.

Koyarwar hadisin: Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ZIKIRAN SAFIYA DA YAMMA · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah