ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci…

Bayanin hadisin: ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya roƙi Allah ya tambaye shi sai ya ce: (Ya Allah Ka shiryar da ni) Ka shiryar da ni Ka nuna mini (Ka datar da ni) Ka yi mini gam da katar, Ka sanya ni madaidaici a dukkan al'amurana.

Shiriya: Ita ce sanin gaskiya a fayyace kuma a dunƙule, da dacewa ga binta a zahiri da baɗini.

Dacewa kuwa: Ita ce dacewa da daidaita a dukkanin al'amura da abinda zai zama daidai akan gaskiya, shi ne hanya madaidaiciya a magana da aiki da ƙudiri.

Kuma cewa umarni na ma'ana yana bayyana da abin ji; ka tina alhali kai kana yin wannan addu'ar cewa: (Shiriya: Shiriyarka (irin ta) hanya) ka halarto zuciyarka alhali kai kana roƙon shiriya kamar shiriyar wanda ya yi tafiya, cewa shi baya kaucewa akan hanya dama da hagu; hakan dan ya kuɓuta daga ɓata (makuwa), da haka ne zai samu kuɓuta, ya kai zuwa manufarsa a gaggauce.

(Daidaita: (irin) daidaitar kibiya) kai kana lura a lokacin da kake daidaita kibiya a gaggawar saduwarta da samunta ga inda aka harbata, mai harbi idan ya harbi inda yake so sai ya daidaita kibiya wajen inda zai harba, to haka nan zaka roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - cewa abinda ka yi niyyarsa na daidai yana kan yanayin kibiya; sai ka zama a roƙonka mai neman matuƙar shiriya, da ƙarshen daidaita.

Ka halarto wannan ma'anar a zuciyarka har sai ka roƙi Allah daidai dan abinda ka yi niyyarsa daga hakan ya zama akan yanayin abinda kake anfani da shi na harbi.

Koyarwar hadisin: ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci…

Rukunan : FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI · ADDU'O'I DA AKA RUWAITO · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.7 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah