Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muham…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun adduoi da zikirai > Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muham…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulun…
Bayanin hadisin: Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulun…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa.
(Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya.
(Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.
Koyarwar hadisin: Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulun…
- Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.
- Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
- Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.
- Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.
- An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.
- Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.
Rukunan :
FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· SAKAKKUN ZIKIRAI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah