Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «كان رجلٌ يُدَايِنُ الناسَ، فكان يقول لفتاه: إذا أتيتَ مُعسِرًا فتجاوز عنه، لعل اللهَ يَتجاوزُ عنا، فلقي اللهَ فتجاوز عنه».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Game da mutumin da ya kasance yana mu'amalar bashi tare da mutane, ko ya siyar bashi, Ya kasance yana cewa yaronsa wanda yake karbo masa basukan dake hannun mutane: Idan ka je wurin wanda ake bi bashi kuma ba shi da abinda zai biya bashin dake kansa dan gajiyawarsa "To ka kau da kai gare shi"; ko dai da jinkirta masa da rashin nace masa a kan ya biya., Ko da karbar abinda ke tare da shi koda tare da abinda ke cikinsa ne na tawaya, hakan dan kwadayi daga gare shi akan Allah Ya ketare masa kuma ya yi masa rangwame. Lokacin da ya mutu sai Allah ya yi masa afuwa kuma ya ketare daga munanan ayyukansa.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA