Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahma…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ الْمُقْسِطِينَ عِنْدَ اللهِ عَلَى مَنَابِرَ مِنْ نُورٍ، عَنْ يَمِينِ الرَّحْمَنِ عَزَّ وَجَلَّ، وَكِلْتَا يَدَيْهِ يَمِينٌ، الَّذِينَ يَعْدِلُونَ فِي حُكْمِهِمْ وَأَهْلِيهِمْ وَمَا وَلُوا».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsu da hukuncinsu da iyalansu, cewa su za su zauna a kan abubuwan zama maɗaukaka haƙiƙa an haliccesu daga haske, don girmamawa garesu a ranar al-ƙiyama. Waɗannan munbarorin suna daman Ubangiji Al-Rahman, kuma su duka hannayensa biyun na dama ne.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA