Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yay…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yay…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi…
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ الشَّدِيدُ بِالصُّرَعَةِ، إِنَّمَا الشَّدِيدُ الَّذِي يَمْلِكُ نَفْسَهُ عِنْدَ الْغَضَبِ».
Bayanin hadisin: Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa ƙarfi na haƙiƙa ba ƙarfin jiki ba ne, ko wanda yake ka da wasu ƙarfafa, kaɗai mai tsananin ƙarfi shi ne wanda yake yaƙar zuciyarsa, kuma yake rinjayarta a lokacin da fushi ya yi tsanani a gareshi; domin cewa wannan yana nuni a kan ƙarfin da zai tabbatar da shi a kan kansa da rinjayarsa a kan Shaiɗan.
Koyarwar hadisin: Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi…
- Falalar haƙuri da kiyaye rai a lokacin fushi, kuma cewa yana daga cikin ayyuka na gari waɗanda musulunci ya kwaɗaitar a kansu.
- Yaƙar zuciya a lokacin fushi shi ne mafi tsanani daga yaƙar maƙiyi.
- Canjawar musulunci ga fahimtar ƙarfi irin na Jahiliyya zuwa ɗabi'u masu girma, to, mafi tsananin mutane a karfi shi ne wanda ya mallaki ragamar kansa.
- Nisanta daga fushi; saboda abin da yake jawowa na cutarwa a kan ɗaiɗaiku da jama'a.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah