Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيَقُلْ خَيْرًا أَوْ لِيَصْمُتْ، وَمَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ جَارَهُ، وَمَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَلْيُكْرِمْ ضَيْفَهُ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa bawan da ya yi imani da Allah da ranar lahira wadda makomarsa take a cikinta, kuma a cikinta sakayyar aikinsa take, to, imaninsa zai kwaɗaitar da shi a kan aikata waɗannan ɗabi'un.
Na farko: Magana mai kyau: Ta tasbihi da hailala, da horo da aikin alheri, da hani daga abin ƙi, da gyara a tsakaknin mutane, idan bai aikata ba, to, ya lazimci shiru, ya kame daga cutarwa, ya kiyaye harshensa.
Na biyu: Girmama maƙoci: Da kyautata masa da rashin cutar da shi.
Na uku: Girmama baƙo mai gabatowa don ziyararka: Ta hanyar daddaɗan zance da ciyar da abinci da makamancin hakan.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA