Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka…
عن جرير بن عبد الله رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ لَا يَرْحَمِ النَّاسَ لَا يَرْحَمْهُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ».
Bayanin hadisin: Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda baya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba, to, jin ƙan bawa ga halitta yana daga mafi girman sabubban da ake samun rahamar Allah da su.
Koyarwar hadisin: Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka…
- Jin ƙai abin nema ne ga sauran ababen halitta, sai dai an keɓanci mutane da ambato ne don ba da muhimmanci garesu.
- Allah Shi ne Mai jin ƙai, kuma Yana jin ƙan bayinsa masu jin ƙai, to, sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki.
- Jin ƙai ga mutane ya tattaro alheri garesu da tunkuɗe sharri garesu da mu'amalantarsu da kykkyawa.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah