Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin…
عن عائشة رضي الله عنها قالت: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إنَّ المُؤْمِنَ ليُدرِكُ بِحُسْنِ خُلُقِهِ دَرَجَةَ الصَّائِمِ القَائِمِ».
Bayanin hadisin: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin…
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana kyawawan ɗabi’u suna kai mai yin su matsayin mai azumi kullun da rana kuma mai Nafila da daddare, matattarar kyawawan ɗabi’u ita ce: bayar da kyakkyawan abu, da kyakkyawar magana, da sakin fuska da rashin cutar da mutane da jure cutarwarsu.
Koyarwar hadisin: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin…
- Girman yadda Musulunci ya kula da tsaftace kyawawan ɗabi’u da kuma cika su.
- Falalar kyawawan ɗabi’u, har suna kai bawa ya samu matsayin mai azumi wanda ba ya hutawa, mai nafilar dare wanda ba ya gajiya.
- Azumi da rana da Nafila da daddare ayyuka ne masu girma, suna da wahala ga rai, amma mai kyawawan ɗabi’u ya kai matsayinsu saboda ƙoƙari da ya yi a kansa da kyakkyawar mu’amala.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· HALAYE NAGARI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أستغفر الله
Ina neman gafara daga Allah