Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sharrinku?

Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sharrinku?

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sh…

Bayanin hadisin: Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sh…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikin wasu mutane cikin sahabbansa suna zaune sai ya tambayesu, shin bana sanar daku in tunatar muku wanda yake shine mafi alherinku da wanda yake shine mafi sharrinku ba? Da ba su yi magana ba kuma basu amsa masa da komai ba, dan jin tsoron banbance alherinsu da sharrinsu, suka ji tsoron kunyata sai suka yi shiru. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake yi musu tambaya sau uku, sai wani mutum daga cikinsu ya amsa: Eh ya Manzon Allah, bamu labarin mafi alherinmu daga mafi sharrinmu. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana musu: Cewa mafi alherinku shine wanda ake sauraro kuma ake fatan (samun) alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ake amincewa sharrinsa dan haka ba'a jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba'a fata kuma ba'a sauraro ba'a kwaɗayin alherinsa da kyautatawarsa da alherinsa, kuma ba'a amincewa sharrinsa, kai ana jin tsoron ta'addancinsa da munanawarsa da kuma zalincinsa.

Koyarwar hadisin: Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sh…

Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.7 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah