Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) …
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku b…
Bayanin hadisin: Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku b…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana alamar shigar watan Ramadan da kuma fitarsa, sai ya ce:
Idan kun ga injirin watan Ramadan to ku azimce shi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwanaki talatin na watan Sha'aban, idan kun ga jinjirin watan Shawwal to ku ajiye azumi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwana talatin ga watan Ramadan.
Koyarwar hadisin: Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku b…
- Dogara a tabbatar da shigar wata akan gani ne ba akan lissafi ba.
- Ibunl Munzir ya cirato ijma'i akan cewa azimi ba ya wajaba idan shigar watan Ramadan ya kasance da lissafi ne kawai ba ganin (wata) ba.
- Wajabcin cika Sha'aban kwana talatin idan girgije ko makancinsa ya tsare ganin jinjirin watan Ramadan.
- Watan sama ba ya kasancewa sai kwana ashirin da tara, ko kwanaki talatin.
- Wajabcin cika Ramadan kwanaki talatin idan girgije ko waninsa ya tsare (ganin) jinjirin watan Shawwal.
- Wanda yake a wurin da babu wanda yake bibiyar al'amarin musulmai a sha'anin azimi, ko akwai wanda bai kula da hakan ba to yana kamata ya kiyaye hakan ya bibiye shi da wanda hakan yake tabbata a wurinsa da ganin kansa ko da ganin wanda ya aminta da shi; sai ya yi azimi da hakan kuma yasha ruwa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· AZUMI
· FIƘHU DA USULU
· Ganin wata
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah