Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan ta…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan ta…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku ding…

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه: أَنَّ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالُوا لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: يَا رَسُولَ اللهِ، ذَهَبَ أَهْلُ الدُّثُورِ بِالْأُجُورِ، يُصَلُّونَ كَمَا نُصَلِّي، وَيَصُومُونَ كَمَا نَصُومُ، وَيَتَصَدَّقُونَ بِفُضُولِ أَمْوَالِهِمْ، قَالَ: «أَوَلَيْسَ قَدْ جَعَلَ اللهُ لَكُمْ مَا تَصَّدَّقُونَ؟ إِنَّ بِكُلِّ تَسْبِيحَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَكْبِيرَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَحْمِيدَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَهْلِيلَةٍ صَدَقَةً، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ صَدَقَةٌ، وَنَهْيٌ عَنْ مُنْكَرٍ صَدَقَةٌ، وَفِي بُضْعِ أَحَدِكُمْ صَدَقَةٌ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَيَأتِي أَحَدُنَا شَهْوَتَهُ وَيَكُونُ لَهُ فِيهَا أَجْرٌ؟ قَالَ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ وَضَعَهَا فِي حَرَامٍ أَكَانَ عَلَيْهِ فِيهَا وِزْرٌ؟ فَكَذَلِكَ إِذَا وَضَعَهَا فِي الْحَلَالِ كَانَ لَهُ أَجْرٌ».

Bayanin hadisin: Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku ding…

Wasu daga talakawa cikin sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku:

Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.

Koyarwar hadisin: Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku ding…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · ZAKKA · FALALOLI · FALALOLIN ZIKIRI · FIƘHU DA USULU · FALALOLI DA LADUBBA · SADAKA TA NAFILA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah