Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai hai…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عبد الله بن عبَّاس رضي الله عنهما قال: «أُمِرَ الناس أن يكون آخر عَهْدِهِمْ بالبيت، إلا أنه خُفِّفَ عن المرأة الحائض».
Dakin Ka'aba yana da daraja da daukaka,kuma shi wata alama ce ta bautar Allah da kankan da kai da tsoron Allah,kuma yana da kwarjini a zukatan mutane,rayuka sun damfaru da shi,suna son shi.Don haka Annabi ya umarci mahajjaci daya sanya dawafi ga dakin Allah abu na karshe,ya zama ban kwana,sai dai anyi sauki ga mace mai haila don gudun kar ta bata masallacin.wannan kuma ya shafi Hajji ne kawai banda Umra.Duba littafin Taisiril Allam,Tanbihul Afham,Ta'asisil Ahkam.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · HAJJI DA UMRA · DA'AWA ZUWA GA ALLAH · FALALAR MUSULUNCI DA KYAWAWAN ABUBUWANSA · FIƘHU DA USULU · SIFFAR AIKIN HAJJI · DA'AWA DA HISBA