Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan z…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن جابر رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «رَحِمَ اللهُ رَجُلًا سَمْحًا إِذَا بَاعَ، وَإِذَا اشْتَرَى، وَإِذَا اقْتَضَى».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da rahama ga dukkanin wanda ya kasance mai sauki mai kyauta a cinikinsa; Ba ya tsanantawa mai saye a farashinta kuma yana mu'amalantarsa da kyakkyawan halaye, Mai sauki mai kyauta idan zai siya, baya tauye mudu kuma ba ya karanta daga kimar haja. Mai sauki mai kyauta idan ya nemi biyan basukansa; ba ya tsanantawa akan talaka da mabukaci, kai yana nemansa da sauki, kuma yana jinkirtawa wanda ke cikin mawuyacin hali.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA